2 Corinthians 6

1A matsayinmu na abokan aikin Allah muna roƙonku kada ku karɓi alherin Allah a banza. 2Gama ya ce,

“A lokacin samun alherina, na ji ka,
a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.”
Ish 49.8

Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto.

Wahalolin Bulus

3Ba ma sa abin tuntuɓe wa kowa, domin kada hidimarmu ta zama abin zargi. 4A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da masifu, 5da shan dūka, da cikin ɗauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa, 6da cikin tsarki, da fahimta, da haƙuri, da kirki, da cikin Ruhu Mai Tsarki, da cikin ƙauna mai gaskiya, 7da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah, muna riƙe da makaman adalci dama da hagu, 8ta wurin ɗaukaka da ƙasƙanci, da cikin ɓata suna, da kuma cikin yabo; cikin faɗin gaskiya, an ɗauke mu masu ƙarya, 9mu da muke sanannu, sai aka ɗauke mu kamar ba a ma san mu ba, kamar a bakin mutuwa muke, ga shi kuwa a raye muke, ana ta horonmu, duk da haka ba a kashe mu ba, 10kamar muna baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke, kamar matalauta, duk da haka muna sa mutane da yawa su azurta, kamar ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.

11Ya ku Korintiyawa, mun yi muku magana a sake, muka kuma saki zuciya da ku ƙwarai. 12Ba mu ƙi nuna muku ƙaunarmu ba, sai dai ku kuka ƙi nuna mana. 13A wannan zance kam, ina magana da ku kamar ʼyaʼyana, ku ma ku saki zuciya da mu.

Kada Ku Haɗa Kai da Marasa Bi

14Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu? 15Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi? 16Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce: “Zan zauna tare da su, in yi tafiya a cikinsu, zan zama Allahnsu, su kuma su zama mutanena.”
L Fir 26.12; Irm 32.38; Ezk 37.27


17“Saboda haka, sai ku fito daga cikinsu,
ku keɓe kanku,
in ji Ubangiji.
Kada ku taɓa wani abu marar tsabta,
zan kuma karɓe ku.”
Ish 52.11; Eze 20.34,41

18“Zan zama Uba a gare ku, ku kuma za ku zama ʼyaʼyana, maza da mata,
in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
2 Sam 7.14; 2 Sam 7.8

Copyright information for HauSRK